Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Kidayar Kuri'u a Kasar Kamaru


Kasar Kamaru ta fara kirga kuri’ar da aka kada a zaben shugaban kasa na ranar Lahadi, wanda jamai’ai da masu sa ido na kungiyar Tarayyar Afrika suka kwatanta da mai inganci.

Hukumomin sun ce an samu yan matsalolin nan da can da ma wasu rigingimu masu alaka da zaben, amma dai basu wani tasiri ba a kan sakamakon zaben.

Yan Kamarun sun koma bakin aiki a ranar Litinin, wuni guda bayan kammala zaben shugaban kasa.

Yayin da ake jiran sakamakon zaben a hukumar nan da makwanni biyu, hukumar zaben Kamaru ta kwatanta zabe da cin nasara.

Erick Essouse, shine babban darekta mai kula da zabe a hukumar zaben kasar. Ya ce an yi zaben cikin ruwan sanyi a wurare da dama a yankunan masu amfani da harshen Ingilishi da na Farasanci.

Ya ce an samu kananan rigingimu a wasu runfunar zabe da ya yi sanadiyar cacar baki tsakanin yan takara daya zuwa biyu da aka samu nan da can wanda ya so ya kawowa harkokin jama’a tsaiko. Irin wadannan cin mutunci basu dace da tsarin demokaradiya da ya baiwa kowa yancin fadar albarkacin bakinsa.

Sama da mutane dubu bakwai ne suka sa ido a kan zaben na Kamaru, ciki har da jami’ai daga kungiyar Tarayyar Afrikan .

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG