Cikin wadanda suka hadu da fushin yan siyasan har da tawagar mukaddashin gwamnan jihar dana 'yan takarar PDP, da SDP.
Yanzu haka an soma musayan kalamai a tsakanin jam’iyyun siyasa, a jihar Taraba, game da harin da ake kaiwa ‘yan takarar yayin gangamin kamfe wanda a wasu lokuta kan jawon hasaran rayuka.
Duk jam’iyyun jihar na zargin juna dagane da hare-haren dake faruwa a wuraren kamfe.
Mukaddashin Gwamnan jihar Sani Danladi, daya ke jawabi kan hare-haren yace an ci masa mutunci, amma yayi hakuri, ya yafewa kowa, yace amma duk wanda yace ba zaiyi biyayya ga Gwamnati ba toh zai gamu da hukuma.