Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

YDG - Ta Yaya Kafofin Sadarwa na Zamani Zasu Taimakawa Shugabanci?


WhatsApp

Batun samun shugabanci na gari na daga cikin batutuwa da suka fi daukar hankulan jama'ar yammacin Afirka, musamman ma ganin cewa babban zaben Najeriya na 2015 na tafi? Ta yaya za'a iya amfani da na'urorin zamani wajen tabbatar da shugabanci na gari? Tambayar shirin Yau da Gobe na Laraba kennan.

Kadan daga cikin amsoshin ku game da “me ya sa maza ke kara aure?”

“Bakincin manyammune. Aisu bakudi sukbiya sukai karatunba dasuma sunyi abinda akaimasu da hakan baifaruba. suburinsu komai acesune. rashin kulawansune yajefamu cikin halindamuke ayanzu. duba kabab cikin yen boko haram ai babu dan wane aciki dukansu yayan talakawane. mudin ba'adaukimatakinda yakamataba wakin hula zaikaimudare Allah ye kyuta.” – Yerema Bunu

“shine daidai.... muda mukaje makarantan wani anfani ta zan mana bancin walakanta zaune a gida .... wadanda sukaki sun samu sana'ar da sukeyi, wasu kuma sun zama manyan yan siyasa sunfimu daraja a gidan gwamnati, sunyi aure ,ga diya ... mu kuwa da mukasa bokon gaba sai zaman rokon kudi da jiron tsamani, munzama abin dariya idon wadanda basuyi ba.... Allah ya wadaran rayuwan wanda yayi boko a nigeria.” – Shuaibu Yusuf

“Idan dalibi ya zana jarabawa ya fadi saikaga ya hakura da karatu saboda bashi da kudin da zai biya yasakeyin wata kuma idan akazana jarabawa ancutar mutane wai sai,ace sai iyawanda gwamnati zasu biyawa iyasu za'ace sunci jarabawa wannan abunma yanabawa dalibai hakura da karatu” – Suleman Sani

A shirin Yau da Gobe na Talata:

Matasa Masu Basira:

Shirin Yau da Gobe ya tattauna da Abdullahi Usman “Maigaskaya,” shahararren mai daukar hoto wanda a kafi sani da “Maigaskiya Photography.” Maigaskiya ya yi bayanin yadda ya ke amfani da matsayin shi na mai daukan hoto ya na taimakawa mata su koyi iya dogaro da kan su.

Abinci:

Halima Abdullahi ta bayyana yadda ake yin kunun goriba.

Tattaunawa da Matasa:

Wakilin mu, Mahmud Ibrahim Kwari, ya kai ziyara kasuwar matasa masu gyaran waya da kuma sayar da ita inda ya tattauna da su game da kalubalen da suke fuskanta wajen koyon aikin gyaran waya.

Tambaya da Ansa:

Kun ko san cewa matasan arewa ba sa samun isasshen taimako a fannin fasahar zamani, duk da cewa kasashen waje na taimakawa? Dakta Mohammed Hashim, masanin na’urar kwamfuta da kafofin sadarwa na zamani ya yi bana bayani da kuma yadda za mu tallafawa matasa wajen amfani da taimakon da kasashen waje ke yi wajen bunkasa fannin fasaha.

Tambayar Ranar Laraba:

A ganin ku, ta yaya za’a iya amfani da kafofin sadarwa na zamani a girka tsarin shugabanci na gari?

XS
SM
MD
LG