Accessibility links

An Fara Taro kan Zaben 2015 a Najeriya


Mazabar "Tarauni Gardens" a Kano ana tantance sunayen masu zabe kafin su fara jefa kuri'unsu a zaben 'yan majalisar dokokin tarayya

Hukumomi da kungiyoyi da jam'iyyun siyasa daga Najeriya da waje sun fara taro a Lagos kan yadda za a hana yin amfani da kudi wajen sayen zaben 2015

Hukumomi tare da kungiyoyi da ma jam'iyyun siyasa na Najeriya sun fara gudanar da wani taron da aka shirya da nufin tabbatar da cewa ba a yi amfani da kudi ko cin hanci domin saye zabubbukan da za a yi a kasar a shekarar 2015 ba.

Wadannan sassa su 11 dake ganawa sun hada har da hukumar yaki da zarmiya da cin hanci ta Najeriya, EFCC, da babbar kungiyar kwadago ta Najeriya, da gamayyar jam'iyyun siyasa da wasu kungiyoyi masu zaman kansu na ciki da wajen Najeriya.

Akasarin wadanda suka yi jawabai a wajen taron su na nuna yatsa ma gwamnati ce domin a cewarsu, ita ce mai wuka da nama a harkokin zaben, kuma ita ce take karkata akalar zabubbuka domin biyan muradunta.

Dr. Inusa Tanko, shugaban gamayyar jam'iyyun siyasar Najeriya yace su na sa ran wannan taro nasu zai yi tasiri domin abubuwan da suke tattaunawa a kai, kuma shi ya sa ma suke goyon bayan gudanar da taro na kasa da aka ce za a yi.

Ga cikakken rahoton da Ladan Ibrahim Ayawa ya aiko mana daga Lagos.

XS
SM
MD
LG