Accessibility links

Gwamna Mai Ci Ya Zargi Tsohon Gwamnan Jihar Gombe Da Almundahana

  • Ibrahim Garba

Alamar jam'iyyar PDP

Gwamna Ibrahim Dankwambo na jihar Gombe na zargin mutumin da ya gada da rub da ciki kan wasu makudan kudade

Gwamnan jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo y ace ya gaya ma hukumar yaki da almundahana da zagon kasa ma tattalin arziki EFCC ta bincike tsohon Gwamna Danjuma Goje saboda wasu makudan kudaden da ya ce ya yi rub da ciki a kansu.

Gwamnan ya fadi hakan ne lokacin da ya ke karbar rahoton kwamitin Fensho na Kananan Hukumomi da kuma na gwamnatin jihar. Ya ce shi da kansa ya baiwa tsohon gwamnan wadannan kudaden lokacin ya na Babban Akanta-Janar na Nijeriya. A halin da ake ciki kuma ikirarin da tsohon gwamna Danjuma Goje ya yi kwanan nan a wata hirarsu da wakilinmu inda y ace shi ne uban duk wani dan PDP a jihar Gombe ya janyo martani.
Wani mazaunin garin Gombe mai suna Abdulkadir Abab, y ace ai dattijo bai sata amma kuma gashi shi Gojen da ke cewa shi dattijo ne, banda tuhumar da yak e fuskanata a kotu an sake gano cewa akwai wata satar makudan kudade da ya yina Naira biliyan biyar da miliyan dari bakwai.

Abdulkadir y ace banda wannan zarge zarge na almundahana da yake fuskanta, tsohon gwamnan ya yi sanadin mutuwar wasu mutane da dama; banda wadanda ya kora ko kuma ya janyo masu ciwuwwuka saboda tozartawa da cin mutunci.

XS
SM
MD
LG