Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Farfado da Sana'ar Saka a Agayawa Jihar Katsina Nigeria


Wani mutum yana saka a Agayawa jihar Katsina Nigeria.

Agayawa wani dan karamin gari ne dake karamar hukumar Ingawa ta jihar Katsina. Akwai kimamin mutane dubu goma dake zaune a wannan gari. Garin kuma yayi fice wajen saka adere, da yin Rigar tsamiya da Rigar saki da Luru bargo ke nan da kuma sakar hula.

Agayawa wani dan karamin gari ne dake karamar hukumar Ingawa ta jihar Katsina. Akwai kimamin mutane dubu goma dake zaune a wannan gari. Garin kuma yayi fice wajen saka adere, da yin Rigar tsamiya da Rigar saki da Luru bargo ke nan da kuma sakar hula. Tun fiye da shekaru arba’in wannan sana’a ke samar da aiyukan yi musamma ga matasa, ga kuma alfanun da ake samu ta fuskar tattalin arziki. Kwanaki na ziyarci wannan gari kuma duk wanda ka gani a garin galibi au yana saka hula ko kuma yana sakan adere ko rigar saki irin ta sarakuna. Mata kuma sune galibi suke yin kadi. Ba Nigeria kadai ba har daga wasu kasashe musamman makwaptan Nigeria ake zuwa sayen adere da rigunan saki da huluna a wannan gari to amma kash a yan shekaru baya, sai wannan sana’a ta durkushe.

To amma sai hukumar samar da aiyukan yi NDE a takaice tare da hadin gwiwar karamar hukumar Ingawa suka farfado da wannan sana’a.

Na zanta da wasu mutane da kuma jami'an da suke da hannu a farfado da masakar kamar Magajin Agayawa Alhaji Idris Yusuf da Mallam Nura Aliyu ‘yan Doma mataimakin shugaban karamar hukumar Ingawa da Mallam Haru mai Luru wanda ya share fiye da shekaru sittin yana wannan sana’a sai kuma Enginiya Yakubu Umar Mani mai kula da wannan cibiya ko kuma masaka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:09:01 0:00

XS
SM
MD
LG