Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fitar Da Jadawalin Zaben Nijar Yayinda 'Yan Adawa Ke Kauracewa Hukumar Zaben Kasar


Ma'aikatan hukumar zaben Nijar
Ma'aikatan hukumar zaben Nijar

Hukumar zabe a jamhuriyar Nijar ta fitar da jadawalin zabubbukan da za a gudanar a kasar domin ba ‘yan siyasa damar fara daura damara tun da wuri, abinda jam’iyya mai mulki ke cewa ya yi daidai a yayin da ‘yan adawa kuwa ke ci gaba da kauracewa ayyukan wannan hukuma da suke yiwa kallon ‘yar amshin shatan gwamnati.

An fitar da jadawalin a kashegarin ganawar da aka yi tsakanin hukumar zabe da masu ruwa da tsaki a harkokin zabe na Jamhuriyar Nijar wanda ya bayyana cewa za a fara da zaben kansiloli a farko shekarar 2020 kafin a cike da 'yan majalisar dokoki da kuma na shugaban kasa a farkon shekarar 2021.

" Za a yi zaben kananan hukumomi a 12 ga watan Janairun 2020, zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa tsakanin Oktobar 2020 zuwa Fabrairun 2021." in Aladuwa Amada, Mataimakin Shugaban hukumar CENI

Jam'iyya PNDS-Tarayya mai mulki sun bayyana gamsuwarsu da tsarin da aka fitar amma jam'iyyar PND Awaiwaya ta ce warware hayaniyar da ke tattare da kundin zabe ne ya kamata a ce Hukumar CENI ta bai wa fifiko ba wai saka ranakun zabe ba.

" To zabennan, a haka yadda ake jami'an tsaro ne za a fito da su don su tsare wasu 'yan kasa su yi zabe amma wasu ba za su yi ba? Su wanene ma tukun 'yan takarar, ko su waye za su yi zaben, kuma su waye ne za a zaba. Kaga wannan abun dubawa ne." inji Shugaban Jam'iyyar PND Awaiwaya, Sumaila Amadou

Ya kara da cewa,

"Babu yadda za a yi a ce hukumar zabe ta shirya zaben muddun ba a je aka gyara wannan kurakurai na kudin zabe ba."

Tun a watan Nuwamba ne mambobin hukumar zabe suka yi rantsuwar kama aiki, amma har yanzu 'yan adawa ba su aika da wakilansu a hukumar ta CENI ba, dalilin da ya mataimakin ya ja hankali game da shi.

"Matsala ce ta siyasa, mu kuma ba kungiyar siyasa ba ce ba hukamar siyasa ba ce face hukumar zabe. Inda mun gano kan matsalar, da mun shawo kanshi. Mu dai fatanmu shi ne, 'yan siyasa sun fahimci juna, kowa yazo mu tsara zabe tare kuma a je a yi zabe tare." inji mataimakin shugaban hukumar CENI

Saurari cikakken rohoton Sule Moumouni Barma

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG