Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gabatar Da Kudurin Dokar Da Za Ta Hana Trump Janye Takunkumin Rasha


 Donald Trump
Donald Trump

Wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka daga manyan jam’iyyu biyu sun gabatar da kudurin doka jiya laraba, wadda za ta hana gwamnatin shugaba Trump janye takunkumin da aka sanyawa Rasha har sai majalisar dokoki ta amince da yin hakan.

Babban dan jam’iyyar Democrat a Kwamitin kula da ayyukan leken asiri na majalisar wakilan Amurka, Adam Schiff, ya ce tattaunawar sirrin da Flynn ya yi da jakadan Rasha a Amurka kan batun takunkumin, kamar yadda aka fallasa cikin kwanakin nan, ta kara muhimmanci ga zartas da wannan doka.

Schiff yana Magana ne a kan tsohon mai ba shugaba Trump shawara kan harkokin tsaron kasa, Michael Flynn, wanda ya yi murabus ranar litinin a saboda matsin lambar da ya biyo bayan fallasar da aka yi ta tattaunawarsa da jakadan Rasha a Amurka tun kafin Trump ya karbi ragamar shugabancin Amurka.

Schiff ya ce ko jami’an gwamnatin Trump suna da masaniya ko ba su da masaniyar wannan tattaunawa da Flynn ya yi da jakadan, bai kamata a kyale wannan shugaban da ikon janye takunkumin da aka sanya ma Rasha shi kadansa ba.

Sai dai kuma shugaban kwamitin leken asirin dan jam’iyyar Republican, Devin nunes, ya ce shi yana sha’awar binciken yadda aka tsegunta ma kafofin yada labarai irin tattaunawar da Flynn ya yi da jakadan na Rasha ne, amma ba wai irin huldar dake tsakaninsa da Rasha ba.

XS
SM
MD
LG