Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Gawarwaki 36 Cikin Wata Rijiya Da Ta Rufta A Wani Wurin Ibada A Indiya 


An gano gawarwakin mutane 36 a cikin wata rijiya a wani wurin ibada na mabiya addinin Hindu da ke tsakiyar Indiya bayan da mutane da yawa da ke halartar wani biki suka fada cikin tabo a lokacin da murfin rijiyar ya rufta, a cewar jami'ai ranar Juma'a. 

WASHINGTON, D.C. - Bidiyon ruftawar rijiyar na ranar Alhamis a wurin ibadar da ke Indore a jihar Madhya Pradesh ya nuna yanayin rudani, inda mutane suka yi ta guduwa.

Wani ma'aikacin hako abubuwa ya balle katangar wurin ibadar wacce aka gina shekaru da dama, don taimaka wa mutane su tsere.

Kusan masu aikin ceto 140, da suka hada da sojoji, sun yi amfani da igiyoyi da tsani wajen fitar da gawarwakin daga rijiyar bayan da suka janye ruwanta. ‘Yar ƙaramar hanya da tarkace a cikin rijiyar sun sa aikin ya zama da wahala.

"Mun fito da gawarwakin mutane 36 kuma an lissafa kowannesu yanzu," abin da Pawan Kumar Sharma, kwamishinan kananan hukumomi, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press kenan.

Sakataren wurin ibadar na daga cikin wadanda suka mutu kuma shugaban wurin na samun sauki daga raunukan da ya samu, in ji Sharma.

-AP

XS
SM
MD
LG