Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Wani Gurbataccen Man Tsaftace Hannu A Najeriya


Hukumar da ke tantance ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC, ta ja hankalin 'yan kasar cewa kasar Amurka ta sanya mayukan tsaftace hannu da aka yi su da barasa na kasar Mexico cikin jerin abubuwan da ta hana shiga da su kasarta.

Hukumar ta NAFDAC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun babban daraktan hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye.

Takwarar hukumar NAFDAC ta kasar Amurka ta ce ta gano yawaitar mayukan tsaftace hannun na kasar Mexico da aka rubuta suna dauke da sinadarin ethanol.

Amma bayan an gudanar da gwaje-gwaje an gano cewa suna dauke ne da sinadarin methanol gurbatacce da ba'a amince da shi ba. saboda yana yi wa fata illa da kuma barazana ga rayuwa idan ya shiga jikin mutum.

Haka kuma yawan amfani da sinadarin kan haifar da cutuka da suka hada da amai, ciwon kai, gani dishi-dishi, makanta, daukewar numfashi a wasu lukutan har da rasa rai.

Hukumar ta NAFDAC ta bukaci masu shigowa, rabawa da kuma sayar da nau'ukan manyukan tsaftace hannun, da su sa ido don ganin an dena sayar da su tare da mika wadanda suke hannunsu ga ofishin NAFDAC mafi kusa.

Ta kuma yi kira ga jama'a da su yi gaggawar zuwa asibiti yayin da suka ji wata alama na rashin jin dadi sakamakon amfani da ko wane irin nau'i na man tsaftace hannu.

NAFDAC
NAFDAC

Shugaban sashen kula da sinadarai na hukumar kula da ingancin kaya (Standard Organisation of Nigeria) ya ce daya daga cikin ayyukan hukumar shi ne, tabbatar da ingancin kayan da al'ummar Najeria za su yi amfani da su kuma agwajin da suka gudanar game da man tsaftace hannu, ba su samu mai dauke da sinadarin Methanol ba.

Wannan dai shi ne karo na farko da humumar Amurka ta fitar da sanarwar hana shiga da duk wani nau'i na magani a duk fadin kasar.

Saurari Rahoto Cikin Sauti Daga Hauwa Umar:

An Gano Wani Gurbataccen Man Tsaftace Hannu A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00


XS
SM
MD
LG