Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gargadi Mazauna Tsibirin Hawai Na Amurka Su Zauna Cikin Gidajensu


Hawaii Volcano

Sanadiyar sabon hayakin da aka ga wani dutsen Kilauea keyi ya sa an gargadi jama'a su zauna gidajensu domin gujewa abun da ya faru watan jiya inda aman wutar duwatsu ya lalata gidaje 467

An gargadi mazauna yankin babban tsibirin Hawaii da ke nan Amurka, da su zauna a cikin gidajensu su kuma kulle tagoginsu, bayan da aka aga dutsen Kilauea, ya sake furzo hayakin toka.

Aman wutar da duwatsun da ya faro tun bayan wata guda, ya mamaye sama da kadada dubu-biyu-da-dari-hudu, ya kuma lalata gidaje 467, ciki har da wani gidan shakatawa mallakar shugaban karamar hukumar Hawaii, Harry Kim.

Hotunan bidiyo, sun nuna rafin narkakken dutse da ya yi jajir ya koma wuta, yana kwarara a wani tsagun kasa da ya shiga yankin da ake kira Kapoho Bay.

An kuma aike da sakon kare lafiya saboda kwararar wutar narkakken dutsen da kuma hazon da ya mamaye sararin samaniya sanadiyar tarururin haduwar wutar dutsen, a lokacin da ta shiga cikin teku.

Wannan lamari na haifar da sinadarin Hydrochloric acid da burbushin duwatsu da ke tashi a sararin samaniyar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG