Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya gayyaci shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un zuwa Rasha domin halartar wani taron kasashen duniya da za’ayi nan bada jimawa ba.

A yau litinin ne Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Rasha Dmitry Peskov ya shaidawa manema labarai a birnin Moscow cewa shugaba Putin ya aika wa shugaba Kim takartar gayyatar ne ta hanyar ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a lokacin da ya kai ziyara Pyongyang a satin da ya gabata.

Peskov yace Putin ya bada shawarar Kim ya halarci taron tattalin arziki na kasashen Gabscin Turai da za a yi a birnin Vladivostok a watan Satumba mai zuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG