Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Girke Jami’an Tsaro Da Dama A Kano Gabanin Daurin Auren Dan Shugaban Kasa

Yusuf Muhammadu Buhari da Amaryasa Zahra Nasiru Ado bayero.

A cewar shugaban kwamitin shirye shirye na bikin Shehu Ahmed za’a kafa tarihi a ranakun Juma’a da Asabar a karamar hukumar Bichi inda za’a daura auren dan shugaban kasa da yar'sarkin garin da kuma nadin sarautar.

A gobe Juma’a ake sa ran daura auren dan shugaban kasa Yusuf Muhammadu Buhari da amaryarsa Zahra Nasiru Ado Bayero, a karamar hukumar Bichi dake jihar Kano.

Tun daga jiya Laraba aka baza jami’an tsaro a ciki da wajen jihar musamman a garin bichi inda za’a gudanar da daurin auren bayan sallar Juma’a.

Shugaba Muhammadu Buhari da wasu hamshakan mutane daga ciki da wajen Najeriya za su halarci bikin, bayan nan kuma a ranar Assabar gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai yi bikin nadin sirikin shugaban kasar wanda shi ne sarkin Bichi

A cewar shugaban kwamitin shirye shirye na bikin Shehu Ahmed za’a kafa tarihi a ranakun Juma’a da Asabar a karamar hukumar Bichi inda za’a daura auren dan shugaban kasa da yar'sarkin garin da kuma nadin sarautar.

Lokacin da tawagar shugaban kasa ta je Kano nemawa Yusuf Buhari auren Zahra a fadar Sarkin Kano a watan Yuni (Facebook/Bichi)
Lokacin da tawagar shugaban kasa ta je Kano nemawa Yusuf Buhari auren Zahra a fadar Sarkin Kano a watan Yuni (Facebook/Bichi)

Ango Yusuf dai ya kasance da namiji tilo ga shugaba Muhammadu Buhari da uwargidansa Aisha Buhari.

Yusuf, dan shekara 27, ya kammala karantunsa ne a jami’ar Surrey da ke Birtaniya, yayin da ita kuma Zahra take kan karatu a jami’ar ta Surrey wacce rahotanni suka ce anan suka fara haduwa.

A ‘yan kwanakin da suka gabata hotunan sharar fagen aurenta suka fita, inda suka janyo ce-ce-ku-ce saboda abin da mutane suka ce, shigar da ta yi, ta sabawa addininta da al’adunta.

Sai dai a hotunan baya-bayan nan da aka fitar, an ga ma’auratan sun dauki wasu hotuna daban da suka yi ta shan yabo a kaffen sada zumunta lura da yadda aka dauke su da kuma irin suturun da suka saka.

Yadda Aka Yi Shagalin Bikin Yusuf Buhari Da Amaryarsa Zahra Nasir Ado Bayero

Yadda Aka Yi Shagalin Bikin Yusuf Buhari Da Amaryarsa Zahra Nasir Ado Bayero
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG