Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Sa An Sake Mayar Da AbdulJabbar Gidan Yari


Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Babbar kotun shari’ar musulinci dake Kofar kudu a tsakiyar birnin Kano ta umarci a ci gaba da tsare Malam Abaduljabbar Nasiru Kabara a gidan gyaran hali zuwa ranar 18 ga watan Agusta mai kamawa.

Bayan ta fara sauraron shari’ar da aka gabatar a gabanta, ana tuhumar malamin da kalaman batanci ga Annabi Muhammad SAW.

A zaman kotun na radar Laraba, karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, Jami’an gidan gyaran halin sun gabatar da Malamin a zauren kotun kuma nan take lauyoyinsa wadanda Barrister Sale Muhammad Bakaro ke shugabanta, sun bukaci kotun ta tilastawa lauyoyin gwamnati su ba su jerin sunayen shaidunsu da kuma sautukan murya da hotunan bidiyo da ake zargin Abduljabbar ya yi wadancan kalamai a cikin su.

Sai dai a martaninta, Barrister Aisha Mahmud dake jagorantar ayarin lauyiyoyin gwamnatin a wannan shari’a ta fadawa kotun cewa, ababubwan da lauya Bakaro ke magana da-ma sauran muhimman takardu da suka shafi wannan tuhuma akan Malam Abduljabbar na cikin kunshin cajin da suka shirya kuma za’a mikawa kotu, wadda zai tabbatar cewa, shari’ar koma hannun gwamnatin jihar Kano daga hannun ‘yan sanda.

Ko da yake, kotun ta gamsu da bayanan Barrister Aisha Mahmud, amma tankiya ta kaure tsakanin lauyoyin bangarorin biyu a zauren kotun, har sai da mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ja kunnensu, tare da tunatar da su cewa, ita kotu fa ba rumfar kasuwa ba ce, a don haka akwai bukatar su girmama juna kuma su kare martabar kotu.

Bayan gamsuwa da bayanan Barrister Amina, daga bisani alkalin kotun ya umarci a mayar da Malam Abduljabbar gidan gyaran hali zuwa ranar 18 ga watan gobe na Agusta, inda za’a ci gaba da sauraron shari’ar.

Barrister Aisha Mahmud dake jagorantar ayarin lauyoyin gwamnati na cewa sun roke kotu ta ba su dama su bayyana chargin a gaban kotu tare da shaidun su, kuma kotu ta karbi rokon.

To amma Barrister Sale Bakaro dake kare Abduljabbar ya bayyana rashin gamsu kan yadda kotun tayi watsi da bukatar su.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

XS
SM
MD
LG