Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Taron Hada Kan Matan Nijer


Nijar: Taron Kungiyar Mata
Nijar: Taron Kungiyar Mata

An gudanar da taro da nufin kara hada kan mata da ‘yan matan kasar Nijar a ci gaba da karfafa matakan kare hakkin mata musamman a fannin siyasa.

Rashin hadin kai a tsakanin matan jam’iyun siyasa ko na kungiyoyin fararen hula wata babbar matsala ce da aka gano cewa tana haddasa cikas ga fafitikar da irin wadanan kungiyoyin suka sa gaba a Nijer don ganin an baiwa mata damar da ke daidai da wace ake baiwa jinin maza wajen tafiyar da al’amuran shugabanci mafari kenan kungiyar FAD ta kira taro don neman mafita inji shugabarta Nafissatou Ide Sadou.

Ta kara da cewa mata na da yawa a nijar kuma abun takaici shine basu da haddin kai, dalilin hada taron kenan.

Matan da suka sami gogewa a fannin siyasa da wasu fitatun matan kungiyoyin fararen hula da ‘yan jarida mata ne suka halarci taron da ke hangen sake jan damarar kwato hakkin mata a fannin siyasa.

Daya daga cikin masu rajin kare dimokradiya irinsu Hadjia Rabi Djibo Magaji ta kungiyar APAISE na kan gaban abinda kira sabuwar tafiyar sha’anin siyasa. Ta kuma kara da cewa maza ba su bane za su kwato ma mata 'yanci ba, mata ya kamata su hada kai su kwato ma kansu.

Tsofafin ministoci mata da wadanda suka taba rike manyan mukaman hukuma a nan cikin gida da waje na bin diddigin wannan yunkuri na kungiyar ONG FAD mafari kenan suka karbi goron gayyata.

Za a ci gaba da shirya makamanacin wannan taro a sauran jihohi 7 na Jamhuriyar Nijer kafin daga bisani a kira babban taron mata na kasa domin cimma matsaya 1 akan yadda mata zasu tunkari babban zaben 2025.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

XS
SM
MD
LG