Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbo Wani Jirgin Soja Mai Saukar Ungulu A Syria


Men inspect the wreckage of a Russian helicopter that had been shot down in the north of Syria's rebel-held Idlib province, Syria August 1, 2016.

A Syria, an harbe wani jirgi soja mai saukar ungulu a Arewa maso Yammacin kasar, dukkan mutane biyar da suke jirgin sun mutu.

Ma'aikatar tsaron Rasha tace jirgin mai jigila an harbo shi ne yayin da yake kan hanyar komawa daga birnin Aleppo inda ya kai kayan agaji, kuma cikin mutanen biyar da suka mutu biyu manyan jami'an soja ne, mutum uku kuma ma'aikatan jirgin ne.


Dakarun Rasha suna kai farmaki da jiragen yaki a Syria a goyon bayan da kasar take baiwa gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.


Tun a shekara ta 2011 'yan tawaye da gwamnatin ta Syria suke fafatawa bayan zanga-zangar lumana ta rikida ta zama yakin basasa.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG