Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Gidauniyar Ilimin Mata A Taron G-7


Mai fafutukar Ilimin mata ta kasar Pakistan Malala Yousafzai,13 ga yuli, 2014.

Firai ministan kasar Canada Justin Trudeau ya sanar jiya asabar cewa an sami alkawuran bada tallafin kudi da ya kai na kimanin dala miliyan dubu dari uku domin ilimantar da ‘ya’ya mata da kuma mata marasa galihu a kasashen duniya.

Canada zata bada gudummuwar dala miliyan dari uku a asusun. Kasashen Jamus da Japan da Birtaniya da kuma babban bankin duniya suna cikin jerin wadanda suka bada gudummuwa ga asusun.

Pirai Ministan ya sanar da haka ne a ranar karshe ta taron kolin kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 da aka gudanar a Quebec.

Kungiyoyin mata da suka gana da Trudeau a gefen taron kolin sun yi maraba da labarin gudummuwar da ta wuce abinda suka zata.

“Wannan zai ba "yammata a kasashe masu tasowa damar neman ilimi a maimakon aure da wuri ko kuma bautar da su.” Inji wadda ta sami lambar yabo ta Nobel Malama Yousafzai, da wadda aka harba a ka a Pakistan sabili da yakin da take yi na ganin ‘yammata sun sami ilimi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG