Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Farmaki Kan Majami'ar COCIN A Jos


Farmaki Kan Majami'ar COCIN A Jos.

Yayin da aka kama wasu matasa su na kokarin kai farmaki kan majami'ar COCIN dake garin Miya-Barkatai a kusa da garin Toro a Jihar Bauchi

An kashe mutane akalla uku a wani harin bam na kunar bakin wake da aka kai cikin mota yau lahadi a wata majami’a dake yankin tsakiyar Najeriya.

Hukumomi sun ce an kai harin na yau ne kan majami’ar COCIN dake garin Jos a Jihar Filato, daga inda wakiliyarmu Zainab Babaji ta aiko mana da wannan rahoton...

Saurari

Rahoton Zainab Babaji Daga JOS

To, ‘yan kilomitoci kadan daga garin na Jos a karamar hukumar Toro mai iyaka da jihar Filato a cikin Jihar Bauchi kuma, jami’an tsaro sun damke wasu matasa dauke da makamai da wasu abubuwan da ake kyautata zaton cewa bama-bamai ne, su na niyyar kai farmaki a kan irin wannan majami’a ta COCIN a kauyen Miya Barkatai.

Saurari

Rahoton Abdulwahab Muhammad Kan Yunkurin Harin Toro

Wadannan al’amura su na zuwa ne a bayan da hukumomi suka kafa dokar hana fita waje baki daya a Gombe, dake arewa maso gabashin kasar, bayan farmakin da aka kai har aka kashe mutane akalla 12 a hedkwatar ‘yan sandan garin ranar jumma’a. ‘Yan sanda ba su tabbatar da ko wadanda suka mutu duka ‘yan sanda ba ne, amma su na tsammanin cewa kungiyar nan ta Boko Haram ce ta kai harin. Hukumomi sun yi nasarar fatattakar hari na biyu da aka kai kan gidan kurkukun garin na Gombe.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG