Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shedu sunce an kashe akalla mutane 20 a Maiduguri


Mutane kewaye da wata bas da irin hare haren da ake kaiwa ya rutsa da ita kwanaki.

Shedu gani da ido a Nigera sune an kashe akalla mutane ashirin a sakamakon fafatawa tsakanin sojoji da yan Boko Haram a Maiduguri

Shehun gani da ido a Nigeria sunce an kashe akalla mutane ashirin a sakamako fafatwar da aka yi tsakanin sojoji da wasu mahara, wadanda ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne, a kasuwar Baga, a Maiduguri, arewa maso gabashin Nigeria.

Mazauna unguwar da jami'an kiwo lafiya sunce yawancin wadanda aka kashen farar hula ne. Kuma an kashe su ne a lokacinda fada ya barke jiya litinin a kasuwar Baga a Maiduguri.

Jami'an soja sun tabbatar da an fafata ama sun musunta cewa an kashe farar hula. Sunce jami'an tsaro su kashe mahara guda takwas kuma sun samu nasarar kwance bama bama da dama da maharan suka daddasa.

Ana kyatata zaton maharan yan kungiyar Boko Haram ne, wadanda suka kaddamar da hare hare a arewacin Nigeria ciki shekara gudan daya shige. Daruruwan mutane aka kashe a irin wadannan hare haren.

Aika Sharhinka

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG