Accessibility links

Sufeto-Janar na 'yan sandan Nijeriya ya yi tir da dabi'ar karbar na goro da kuntatawa jama'a

  • Ibrahim Garba

Wasu 'yan sandan Nijeriya a bakin aiki

Sabon babban jami’in ‘yan sandan Najeriya yace

Sabon babban jami’in ‘yan sandan Najeriya yace ‘yan sandan kasar su na karkashe mutane haka siddan a wasu lokutan, su na daure mutanen da ba su aikata laifin komai ba, su na kuma karbar cin hanci.

A lokacin wani jawabinsa a Abuja, mai rikon mukamin sufeto-janar na ‘yan sanda, Mohammed Abubakar, yace martabar rundunar ‘yan sandan kasar ta zube a kasa warwas.

Sabon sufeto-janar na ‘yan sandan yace bataliyoyin ‘yan sanda da ake kafawa domin yakar fashi da makami sun zamo kungiyoyin kisan kai, kuma ana tsare da mutanen da ba su aikata laifin komai ba a saboda sun kasa biyan kudaden haramun na beli.

Ya bayarda umurnin a saki dukkan wadanda ake tsare da su ba tare da hujja ba, a kuma kawar da dukkan shingayen da ‘yan sanda ke kafawa a kan tituna, watau Rodblok, wadanda akasarin ‘yan Najeriya ke dauka a zaman tungayen tara kudaden cin hanci kawai.

A lokacin da yake magana a gaban wasu jami’an ‘yan sanda da na tsaro, Abubakar yayi alkawarin aiwatar da manya kuma muhimman sauye-sauye domin takalar zarmiya da wuce gona da iri da nufin maido da martabar rundunar a idanun jama’a.

A watan da ya shige shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya nada Abubakar a zaman sufeto janar bayan da ya tilastawa tsohon sufeto janar da dukkan mataimakansa suka yi ritaya.

Shugaban yana shan matsin lamba a kan ya kawo karshen hare-haren kungiyar nan ta Boko Haram.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG