Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hare-haren Kunar Bakin Wake a Birnin Damascus


Wani yankin Syria da aka kai hari

Mutane da yawa sun rasa rayukansu sanadiyar hare-haren kunar bakin wake da aka kai a birnin Damascus na kasar Syria.

A harin farko, mutane kamar 25 suka hallaka, a cewar kamfanin dillacin labaran Syrian, yayin da a hari na biyu da aka kai kamar sa’oi biyu bayan na farkon, wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a wani kantin sayar da abinci dake yammacin birnin na Damascus.

A harin na biyu shima, mutane da dama da ba’a kayyyade yawansu ba, suka mutu.

Wadanan hare-haren na zuwa ne kamar mako daya bayan faruwar wasu makamantansu da aka kai a wata makabartar ‘yan Shi’a, inda akalla mutane 40 suka rasa rayukkansu, kana wasu kamar 120 suka ji raunukka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG