Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Harin Bamabamai da Bindigogi Gaban Barikin Sojoji dake Gombe


Harin bam

Yayin da shekarar dubub biyu da sha hudu ke shudewa 'yan kunar bakin wake da 'yan bindiga sun farma barikin sojoji dake Gombe

Ana gap da yin sallama da shekarar 2014 sai mahara da 'yan kunar bakun wake suka bada goron sabuwar shekara.

Sun kaddamar da kunar bakin wake inda suka tayar da bamabami da harba bindigogi a kofar barikin sojoji dake garin Gombe. Bincike ya nuna cewa 'yan kunar bakin waken da 'yan bindigar basu samu nasarar shiga cikin barikin ba.

Wasu ganao sun ce bam na farko da ya fara tashi wani kuma ya biyo shi kana sai harbe harbe. Babu tabbacin ko mutane sun rasa rayukansu ko kuma sun jikata. A cikin garin Gombe kuwa mutane na ta gudu suna neman mafaka. Amma wani dake kusa da wurin yace ya ga gawar dan kunar bakin wake guda da ta soja guda.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG