Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kakkabo Wani Jirgi Mai Saukan Ungulu a Libya


Bernardino Leon manzon Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Libya

A kasar Libya wani jirgi mai saukan ungulu dake dauke da jami'an gwamnatin 'yan Islama da suka kwace Tripoli ya rikito kasa kuma ya kashe duk wadanda suke cikinsa

An kakkabo wani jirgin sama mai saukar Ungulu jiya, jirgin da yake dauke da wasu daga cikin ‘yan gwamnatin Islama ta Libya mai matsuguni a Tripoli

Ba bayanin ko mutane nawa ne a jirgin amma jami’ai sun ce ba sa sa ran akwai wanda ya tsira a cikinsu.

Masu ra’ayin Islamar sun zargi gwamnatin da suke adawa da ita da laifin harbo jirgin, wanda su kuma suka musanta wannan zargi.

Libya dai ta dare gida biyu tsakanin gwamnatin masu zafin kishin Islama da suka kwace ikon Tripoli da kuma gwamnatin da duniya ta amince da ita a kasar da suka tare a Tobruk.

Zuwa yanzu dai yunkurin Majalisar Dinkin Duniya na hada kan gwamnatocin ya faskara. Libya dai na fama da rikici da rashin daidaiton siyasa tun bayan hambarar da mulkin kama karyar Moammar Gadhafi da aka kashe a shekarar 2011.

XS
SM
MD
LG