Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Dalibai 80 Da Ake Zargi Da Satar Jarabawa A Nijar


A Jamhuriyar Nijar 'yan sanda sun kama wasu gomnan dalibai a birnin Yamai saboda zarginsu da yunkurin sata a jarabawar BAC ta ajin karshen kammala makarantun share shiga jami'a da aka gudanar a makon jiya a fadin kasar.

Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike domin zakulo masu hannu a wannan haramtacciyar haraka dake iya zama sanadin zaman gidan yari shekara 1 zuwa 3 hade da biyan tarar jika 100 na cfa zuwa jika 500 har da dakatarwa daga rubuta dukkan wata jarabawa a kasar na tsawon shekaru.

Kimanin dalibai 80 ne aka kama a nan yamai cikinsu har da 'yan mata 15 wadanda ake zargi da sata a yayin jarabawar BAC din da aka rubuta a fadin Nijer a makon jiya.

A yanzu haka wadanan yara na tsare a hannun hukumar 'yan sandan farin kaya a ci gaba da binciken wannan al'amari kamar yadda kakakin kungiyar dalibai ta USN Effred Hassan ya bayyana bayan da suka ziyarci wadanan abokansu.

Kungiyar uwayen yara dalibai wato APEEN ta nuna damuwa game da faruwar wannan al’amari.

Mataimakin shugaban reshen kungiyar na yankin Yamai Ibrahim Nalado na ganin bukatar a yiwa wadanan yara afuwa amma da sharadi.

Da ma tun a jajibirin ranar fara wannan jarabawa ta BAC dake bada damar samun takardar shaidar kammala makarantun share fagen shiga jami’a hukumar yaki da cin hanci HALCIA da ofishin ministan ilimi mai zirfi, sun sanar da tsaurara matakan zuba ido da nufin dakile yunkurin sata da murdiya tare da tunatarwa akan hukuncin dake hawan kai dukkan wadanda aka kama cewa aikata irin wannan danyen aiki.

A yanzu haka an fara fitar da sakamakon wannan jarabawa a wasu daga cikin ciniyoyi kalilan abinda ya sa wasu ‘yan kasa ke kira a kara zuba akan aiyukan tantance abubuwan da daliban suka rubuta domin tabbatar da gskiya da adalci.

XS
SM
MD
LG