Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Daruruwan Matafiya Daga Jihar Jigawa a Jihar Rivers


Birnin Fatakwal, daga jirgin sama
Birnin Fatakwal, daga jirgin sama

'Yan sanda a Rivers sun tsare mutanen ne da suka fito daga Jihar Jigawa bisa zargin cewa watakila su na da alaka da kungiyar Boko Haram

'Yan sanda a jihar Rivers dake kudancin Najeriya, sun tsare wasu mutane kimanin dari hudu, wadanda suka fito daga yankin arewacin Najeriya, jim kadan a bayan da suka isa birnin Fatakwal.

Wadannan mutane maza da mata, sun fito ne daga jihar Jigawa, kuma sun isa can a cikin wasu motocin bas-bas.

Hukumomin 'yan sanda sun tsare su bisa zargin ko su na da alaka da kungiyar Boko Haram, amma shugabannin al'ummar arewacin Najeriya a Fatakwal sun ce wannan zargin ba ya da tushe.

Wata mace daga cikin wadanda aka tsare ta fadawa wakilin Muryar Amurka, Lamido Abubakar Sokoto, ta wayar tarho cewa an binciki duk kayansu, da motocinsu da kuma jikinsu, amma babu wani abu da aka samu wanda yayi kama ko ya alakanta su da wani abinda ba na halal ba.

Haka kuma, an dauki hotunan yatsunsu, amma har yanzu ba a sake su ba.

Kwamishinan 'yan sanda a Jihar Rivers, ya tabbatar da tsare mutanen, amma ya ki yarda yayi karin haske kan dalilin da yasa har yanzu ake ci gaba da tsare su.

Shugabannin al'ummar Arewacin Najeriya a Fatakwal sun tafi ofishin 'yan sandan inda suka ce ba zasu ja ba har sai sun tabbatar da an bi kadin wannan lamarin.

An Kama Daruruwan 'Yan Jigawa a Rivers da Sunan Boko Haram - 3:02
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG