Accessibility links

'Yan Najeriya Fiye Da Dubu 6 Sun Yi Gudun Hijira Zuwa Kamaru Da Nijar


Wasu 'yan Najeriya da suka yi gudun hijira daga rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya lokacin da suka isa Abuja ranar 4 Janairu, 2014

Hukumar Kula Da 'Yan Gudun Hijira Ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutanen sun gudu ne cikin kwanaki 10 da suka shige a sanadin hare-haren Boko Haram

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce 'yan Najeriya su fiye da dubu 6 ne suka tsere daga gidaje da garuruwansu cikin kwanaki 10 da suka shige, suka nemi mafaka a kasashen Kamaru da Nijar.

Hukumar ta ce 'yan gudun hijirar su na tserewa ne daga hare-haren da kungiyar nan ta Boko Haram ta zafafa kaiwa a kauyuka da karkara, musamman a cikin Jihar Borno wadda take iyaka da kasashe uku: Nijar, Chadi da Kamaru.

Koda a cikin wannan makon ma kawai, 'yan bindigar kungiyar sun kai hare-haren da suka kashe mutane da dama a kauyuka na jihar.

Wannan yana zuwa a daidai lokacin da sabon babban hafsan hafsoshin sojan Najeriya, Air Marshall Alex Badeh, yake alwashin cewa zasu iya ganin bayan kungiyar Boko Haram nan da watan Afrilu, watau watanni uku masu zuwa.

Air Marshall badeh ya fadawa Muryar Amurka cewa mayakan sama su na tallafawa sojojin kasa sosai wajen yin luguden wuta a kan duk wuraren da tsagera suka yi sansani cikin dajin Sambitsa.

Sai dai masana tsaro da dama da kuma dattawan arewa su na ganin kamar wannan alkawarin babban hafsan bai sha bambam da wadanda sojoji da hukumomi suka sha yi a baya ba.

Dr. Bawa Abdullahi Wase da kuma Barrister Solomon Dalung na kungiyar dattawan Arewa, sun ce ba su tsammanin wannan alkawari na Air Marshall Badeh zai sauya abubuwan da suke faruwa a kasa, inda talakawa suka fi shan ukubar wannan yaki.

XS
SM
MD
LG