Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu Matasa Biyu Dauke Da Bam a Jihar Imo


Jihar Imo

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Imo ta kama wasu mutane biyu dauke da bam a garin Orlu, dake yammacin jihar, yayin da ake zargin zasu wani bangaren garin ne domin su tada shi.

Da yake bayyanawa Muryar Amurka yadda lamarin ya faru, babban limamin masallacin Orlu, mallam Abubakar Musa, ya ce mutanen biyu sun je bakin masallaci akan babur ganin yawan jama’ar dake gurin yasa suka hau babur dinsu suka tafi.

A kan hanyarsu ne jami’an ‘yan sanda suka tare su domin bincikarsu sai daya daga cikin mutanen biyu ya fadawa ‘yan sandan cewa shi jami’in soja ne, inda nan take suka nemi katin shaidar aiki, amma babu.

Lokacin da ‘yan sandan suka karbi jakar dake hannu guda daga cikin mutanen biyu, nan take suka gano cewa bam ne.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin kwamishinan ‘yan sandan jihar Mallam Dasuki Galadanci, ya ce yanzu haka sun mika bam din gas ashen dake warware bama-bamai domin gano abubuwan da aka hada bam da shi.

Haka kuma hukumar ‘yan sandan jihar Imo na gudanar da bincike domin gano daga inda aka hada bam din da kuma masu hannu a wannan lamarin.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Alphonsus Okoroigwe.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:08 0:00

Facebook Forum

Ramaphosa Ya Kai Ziyara Najeriya

Lokacinda Ramaphosa Ya Isa Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG