Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wata Ma’aikaciya Da Laifin Neman Na Goro A Filin Tashin Jirage Na Legas


Filin tashin jirage na Murtala Muhammad da ke Legas (Facebook/FAAN)
Filin tashin jirage na Murtala Muhammad da ke Legas (Facebook/FAAN)

"An mika ta ga jami'an tsaro don su dauki matakin da ya dace, saboda hakan ya zama aya ga sauran baragurbi." Sanarwar ta ce.

Hukumar kula da filayen tashin jiragen sama ta Najeriya FAAN, ta dakatar da wata ma’akaciyar "kamfanin Arik Airline" daga aiki bayan da aka zarge ta da laifin neman na goro a hannun fasinja.

Cikin wata sanarwa da Janar-Manaja ta FAAN Henrietta Yakubu ta fitar a ranar Laraba, hukumar ta ce an mika ma’akaciyar ga jami’an tsaro don su dauki mataki a kai, tana mai cewa an kuma karbe bajen aikin ma’akaciyar.

“Hotunan bidiyo da ke yawan yawo a kafafen sada zumunta a kwanan nan da ke nuna ma’aikata suna karbar na goro a hannun fasinja, ya sa ya zama dole a bullo da wata dabara don magance wannan matsala.” In ji Henrietta.

"An mika ta ga jami'an tsaro don su dauki matakin da ya dace, saboda hakan ya zama aya ga sauran baragurbi." Sanarwar ta ce.

An dauki matakin dakatar da ma’akaciyar ne bayan wani taron gaggawa da aka gudanar inda aka tattauna kan yawaitar matsalar korafe-korafen da fasinja ke yi cewa ma’aikata na karbar na goro a hannunsu cewar FAAN.

“Taron ya cimma matsayar cewa daga yanzu, duk ma’akacin da aka kama da laifin neman a ba shi kudi a wani filin tashin jiragen Najeriya, za a hana shi shiga filin tashin jiragen har abada.”

Sanarwar ta Henrietta ta kara da cewa, daga yanzu, an ba ma’aikata umarnin su rika saka bajen da zai rika nuna sunayensu a duk lokacin da suke bakin aiki.

XS
SM
MD
LG