Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wata 'Yar Kasar China A Gidan Hutawa Na Shugaban Amurka


An kama wata mace ‘yar kasar China bayanda ta kutsa cikin jerin gidajen hutawa na shugaban Amurka Donald Trump dake jihar Florida, inda kuma aka same ta dauke da wata na’urar komputa mai lahani a cikinta.

Bayanan da lauyoyin dake shigar da kara suka gabatar, sun nuna cewa wannan matar mai suna Yujing Zhang ta shiga wannan sansanin gidajen na Mar-a-Lago ne dake Palm Beach, tace ita memba din kulob din ce kuma tana son shiga wurin wanka na kulob din.

Duk da cewa masu tsaron wurin basu gano sunanta a jerin sunayen ‘yan kulob din ba, sun barta ta shige da yake daya daga cikin manajojin wurin ya dauke ta a matsayin ‘yar wata mace wacce ita memba ce ta wurin.

Sai dai kuma bayan Yujing ta shiga gun, sai ta chanja bayaninta, tace wai ta zo ne don ta halarci wani taro kan batun tatalin arziki a tsakanin Amurka da China. Bayanda aka gano cewa ba wani taron irin wannan ne aka tsare ta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG