Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Taron Bita Ma Wakilan Muryar Amurka


An kamalla taron bitar kwanaki biyu da Muryar Amirka ya shirya wa wakilan sa a Abujan Nigeria.

Wakilin sashen Hausa a Abuja Nigeria, Hassan Maina Kaina ya aiko da rahoton cewa an kamalla taron bitar kwanaki biyu da Muryar Amirka ya shirya wa wakilan sa da suke Nigeria.

A jawabin data gabatar Malaman Inna, daya daga cikin wadanda suka jagoranci bitar tace makasudin taron shine domin tabatar da wakilan Muryar Amirka na rubuta labarai kan kiwon lafiya da illimi ta hanyar haduwa da mutane da kuma sada su da juna, saboda tsarin aikin yana canjawa da gaggawa a wannan zamanin na'urar internet.

Tace akwai bukatar wakilan Muryar Amirka da su tabbata masu sauraro na fahimtar mai ake magana akai domin suma suna tattauna irin batutuwan da suke sauraro tare da iyalai da kuma abokan arziki.

Tunda farko a jawabin daya gabatar, shugaban sashen Hausa Leo Keyen ya baiyana irin canje canjen da sashen Hausa na Muryar Amirka yake fuskanta domin ya dace da wannan zamani.

Wakilan sashen Hausa da suka halarci taron, sun yabawa wannan yunkuri na kara illmantar da wakilan sashen Hausa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG