Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Ceto Yara Hudu a Thailand


Motar jinya da jirgin sama mai saukar ungulu ne suka dauki yaran da aka ceto zuwa asibitin Chiang Rai, inda aka bayyana cewa basa cikin mummunan yanayi.

Hukumomin kasar Thailand sun ce an samu nasarar zaro karin yara hudu a yau Litinin, daga cikin yaran da suka share fiyeda makkoni biyu makalle a cikin wani kogo.

Wadannan hudun zasu hade da wasu hudu na farko da aka fito da su tun daga jiya, daga jimillar yara 12 ‘yan wasan kwallon kafa da suka makalle a cikin kogon.

Yanzu dai an ja burki ga aikin na yau Litinin, na kokarin da ake na ci gaba da neman sauran yara 4 da mai horad da su (watau Kochi) da suka rage a cikin wannan kogon mai suna Luang Tham.

An dai yi ta sowa da murna a lokacin da mukadashin gwamnan jihar Chiang Rai, dake kasar Thailand, Narongsak Osatanakorn, ya sanar jiya Lahadi cewa an fito da wasu yaran daga kogon.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG