Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Masu Zanga Zangar Adawa Da Joseph Kabila Har 44


Wata kungiyar rajin kare hakkin dan Adam ta ce an kashe mutane akalla 44 a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a tashe-tashen hankulan da aka yi cikin kwanaki biyu, sanadiyyar zanga-zangar adawa da Shugaba Joseph Kabila.

Kungiyar rajin kare hakkin dan adam ta Human Right Watch ta ce ta samu 'sahihan bayanai' cewa jami'an tsaro sun kashe mutane akalla 37 tun da aka fara zanga-zangar ranar Litini.

Shugabar Sashin Binciken kungiyar a Congo, Mrs. Ida Sawyer, ta gaya ma Muryar Amurka cewa akasarinsu an kashe su ne lokacin da jami'an tsaro su ka bude wuta kan cincirindon masu zanga-zangar. Ta ce an kashe sauran ne lokacin da wasu mutane dauke da makamai su ka banka wuta ma hedikwatocin jam'iyyun adawa da dama.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce ta kuma samu rahotanni masu tushe cewa, masu zanga-zanga sun kashe 'yan sanda akalla shida da kuma wani magoyin bayan Kabila, tare kuma da wawushe wasu kantuna da caji'ofis din 'yan sanda da dama.

Jami'an gwamnati sun ce adadin wadanda su ka mutun 17 ne, ciki har da 'yansanda uku da farar hula 14.

Ranar 19 ga watan Disamba ne wa'adin Kabila na biyu zai kare.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG