Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarihin Tsohon shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi


Tsohon shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi a wani taron manema labarai. Feb. 5, 2001,

Moammar Gadhafi ya hau karagar mulkin kasar Libya tun yana saurayi dan shekaru 27 da haihuwa bayanda ya hambarar da gwamnatin sarki Idris a wani juyin mulki na soja a shekarar 1969

An haife Kanar Gadhafi a shekarar 1942 kuma, bayan ya kamalla karatunsa a babbar Jami’ar Libya ne ya shiga aikin soja.

Moammar Gadhafi ya hau karagar mulkin kasar Libya tun yana saurayi dan shekaru 27 da haihuwa bayanda ya hambarar da gwamnatin sarki Idris a wani juyin mulki na soja a shekarar 1969.

Bayan ‘yan shekaru da hawa karagar mulki, Kanar Gadhadfi ya kafa wani tsarin mulki da ake kira a larabci Jamahiriya watau gwamnatin talakawa wadda bisa ga tsarin, shugabannin al’umma zasu gudanar da harkokin mulki, yayinda shi kuma ya dauki sunan shugaban ‘yan’uwa da kuma jagoran juyin juya hali, sai dai a zahiri, ya murkushe ‘yan hamayya yayinda rahotannin suke nuni da cewa, ya sha tsallake rijiya da baya a yunkurin hallaka shi da aka yi da dama.

Gadhafi yayi kaurin suna a duniya saboda halayensa na ba-zato, ba tsammani, da dabi’ar sanya tufafi iri-iri masu ban al’ajabi da suka hada harda kayan da aka yi daga fatun dabbobi, sannan kuma da dabi’ar kai-da-kawo tare da dogarawa mata matasa.

Haka kuma marigayi shugaba Gadhafi, wanda tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan ya taba yi wa lakabin “mahaukacin karen yankin Gabas ta Tsakiya”, yayi suna a duniya saboda irin kalamansa da sauran take-takensa na siyasa wadanda kan janyo kacce-nacce.

Ya sha bada goyon baya ga kungiyoyin juyin-juya hali na kasashen duniya da dama da suka hada da na Chad da Iran. Kuma an sha zarginsa da bada tallafi ga kungiyoyin kishin addinin Islama da wasu kungiyoyin da ake ganin masu akidar ta’addanci ne.

A shekarar alib da dari tara da tamanin da shida, shugaban Amurka Ronald Reagan ya bada umarnin kaiwa kasar Libya harin sararin sama bisa zargin hannun gwamnatin kasar Libya da kai harin bom kan wani gidan rawan kasar Jamus da ya yi sanadin kashe Amurkawa biyu, aka kuma kashe ‘yar rikon Mr. Gadhafi a sumamen da Amurka ta kai.

Bayan shekaru kadai, aka dorawa kasar Libya alhakin harin da aka kaiwa jirgin sufurin Pan Am lamba 103 kan garin Lockerbie na kasar Scotland da ya yi sanadin mutuwar mutane 270. A shekara ta dubu biyu da uku Mr. Gadhafi ya dauki alhakin kai harin ya kuma amince da biyan dangin mamatan diyar dala biliyan biyu.

A wannan shekarar kuma, shugaban kasar Libyan ya amince ya yi watsi da ta’addanci da kuma makaman kare dangi, abinda ya bada damar cire takunkimin da Amurka da kuma kasashen turai suka kakabawa kasar Libya bayan harin da ake zargin kasar da kaiwa kan wani dakin rawar kasar Jamus, aka kuma sake kulla huldar diplomasiya da kasar. Majalisar Dinkin Duniya kuma ta dage takunkumin da ta kafawa kasar dangane da harin Lockerbie.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG