Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Uku a Zauren Taron Yahudawa


Terry Lee Loewen, mutumin da ake zargin ya kashe mutane uku a zauren taron yahudawa.
Terry Lee Loewen, mutumin da ake zargin ya kashe mutane uku a zauren taron yahudawa.

An kama wani mutum a jihar Kansas ana zarginsa da kashe mutane uku a zauren taron yahudawa

Hukumomi a jihar Kansas dake tsakiyar Amurka sun ce an kama wani mutum kan zargin ya kashe mutane uku aharabar gidaje d a zauren taron yahudawa wadnada suka yi ritaya.

Jami’ai a jihar sun fadawa manema labarai sa’o’I bayan harbin da aka yi a wani kauye da ake kira Overland Park, cewa garaje ne a yi saurin danganta mutumin da ake zargi da harbin dan shekaru 70 da haifuwa a zaman makiyin yahudawa.

Baturen ‘Yansandan yakin John Douglas, ya kira lamarin “mummunar aikin tarzoma:, duk da haka yace ana bukatar karin bayani kamin a kira lamarin da cewa an aikata shi ne saboda tsagoran kiyayyar wani jinsi.

Shugaban Amurka Barack Obama ya nuna bakin cikinsa kan aukuwar lamarin, daga nan ya bayyana goyon bayansa dana mai dakinsa ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su.
XS
SM
MD
LG