Accessibility links

Wasu Daliban da Aka Sokawa Wuka na Cikin Mawuyacin Hali


Alex Hribal dalibin da ya sossoki dalibai da wuka.

Kwanaki uku ke nan da wani dalibi dan shekara 16 ya sossoki dalibai 19 da wuka a jihar Pensylvania ta kasar Amurka. Likitoci sun bayyana cewa wasunsu na cikin halin rai kwakwai mu kwakwai

Likitoci a jihar Pennslyvania gabashin nan Amirka sunce dalibai guda biyar, suna cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai, kwana daya bayan da wani dan ajinsu ya kai musu hari da wuka a makarantarsu.

Hukumomi sun caji yaron da ya aikata wannan dayen aiki, mai suna Alex Hribal dan shekara goma sha shidda da haihuwa da laifin aikata laifuffuka guda hudu na yunkurin kisa da kuma laifin kai mumunan hare hare ashirin da daya a harin daya raunana mutane ashirin da biyu.

Jami'ai sun baiyana cewa a ranar Laraba, jim kadan kafin a fara karatu a makarantar sakandaren Franklin Regional a garin Murrysville kusa da birnin Pittsburgh, Alex wanda, dauke da wukake guda biyu ya yi ta sosoke yan makaranta ko kuma 'yan ajinsu ba ji ba gani.

A wata hira da gidan talibjin na ABC yayi dashi, lauyan Alex Patrick Thomassey yace yana son masana kiwo lafiya su yiwa Alex Hribal gwaje gwaje a gani ko yana da tabin hankali. Lauyan nasa Patrick Thomassey yace bai san abinda yasa Alex yayi wannan barna ba.
XS
SM
MD
LG