Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Tsohon Shugaban Yamal Ali Abdullah Saleh


Ali Abdullah Saleh
Ali Abdullah Saleh

Jam’iyar tsohon shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh ta tabbatar jiya Litinin cewa an kashe shi, yayin da ake yayata wani faifan bidiyo a kafofin sadarwa da ake cewa gawarsa ce.

“An kashe shi, sabili da kare kasarsa” in ji Faiqa al-Sayyid, shugaban jam’iyar General People’s Congress, wanda ya dorawa ‘yan tawayen dake tada kayar baya alhakin kashe Saleh a Sana’a babban birnin kasar.

Saleh dan shekaru saba’in da biyar, ya mulki Yemen na tsawon sama da shekaru talatin kafin aka hambare gwamnatinsa yayin boren da aka yi a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu da , sai dai ya ci gaba da yin tasiri ta bayan fage, inda ya kulla abota da kungiyar Houthi da Iran ke marawa baya.

Ya mutu kwanaki biyu bayan nuna alamar rugujewar hadin kan. Ranar asabar Saleh ya sanar da raba gari da kungiyar Houthi ya kuma ce zai sake kulla dangantaka da kasar Saudiya.

Yemen
Yemen

‘yan tawayen da suka sanar da mutuwarsa jiya, sunce yana kan hanyarsa zuwa Saudiya ne lokacin da aka kashe shi, suka kuma bayyana mutuwar tasa a matsayin abinda suka kira ‘watsi da dangantakar da bai yarda da ita ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG