Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tura Sojoji Maiduguri, babban birnin Jihar Borno,Domin Karin tarzoma Da Ake Aza Laifin kan 'Yan Kungiyar Boko Haram


Sakamakon karin kisan gilla kan jami'an tsaro da sauran jama'a,rundunar sojan Najeriya ta tura dakarunta zuwa jihar domin magance wan nan matsala.

Rundunar sojan Nigeria ta tura sojoji Maiduguri inda aka dorawa yan kungiyar Boko Harumne laifin karkashe mutane da ake yi.

Shedun gani da ido sunce a jiya talata da dare sojoji suka fara lura da wurare a duk fadin birnin. A ranar litinin yan kungiyar Boko Harum ne suka kai hari wani ofishin yan sanda suka kona shi. Haka kuma hukumomi sun dorawa yan kungiyar laifin kashe wani Malamin daya caccake su a wani shirin gidan rediyo.

Wadannan hare hare yasa ana bayyana fargaban cewa kila yan Boko Haram ne suka sake hada karfin su, bayan da bara, aka yi mako guda ana fafatwa dasu har aka kashe fiye da mutane dari bakwai.

XS
SM
MD
LG