Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Mikel Obi A Matsayin Mai Ba Da Shawara A Fannin Wasanni A Jihar Filato


Mikel Obi
Mikel Obi

Shi dai Obi a birnin Jos ya girma, kuma ya fara wasan kwallonsa ne a garin inda daga baya ya shahara.

Gwamnan jihar Filato Caleb Muftwang ya nada tsohon kyaftin din tawagar Super Eagles ta Najeriya Mikel Obi a matsayin mai ba shi shawara kan sha’anin wasanni.

Wata sanarwa da Darektan yada labarai a fadar gwamnatin Filato Gyang Bere ya fitar ne ta bayyana hakan.

Shi dai Obi a birnin Jos ya girma, kuma ya fara wasan kwallonsa ne a garin inda daga baya ya shahara.

Baya ga rike mukamin kyaftin da ya yi a tawagar Super Eagles ta Najeriya, Obi ya taka leda a kungiyar Chelsea a gasar Premier League ta Ingila.

Ya fara wasanninsa ne tare da Plateau United daga nan ya koma Lyn ta kasar Norway a 2004 inda ya dangana da Chelsea a 2006.

Shekarunsa 11 a Chelsea.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG