Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansanda Sun Kubutadda Uban John Micael Obi Da Ake Garkuwa Dashi


Hoton 'yan wasan kungiyar kwallon kafa na Chelsea, ciki har da John Obi, na farko daga hanun dama.

An sako uban John Obi Mikel dan wasan kwallo kafan nan da aka kama mahaifinsa da aka yi garkuwa dashi, bayan wani somame da ‘yansanda suka kai cikin birnin Kano.

An sako uban John Obi Mikel dan wasan kwallo kafan nan da aka kama mahaifinsa aka yi garkuwa dashi, bayan wani somame da ‘yansanda suka kai cikin birnin Kano.

Jiya litinin suka bada labarin an kama mutanen da suka kama Michael Obi. ‘Yansanda suka ce ba a biya ko sisin kwabo na kudin fansa ba.

Kamfanin kayan nishadi a fannin wasanni dake kula da muradun John Obi ya tabbatar da an saki uban nasa. Shi dai John Obi yana wasa ne da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake ingila ne.

A Jos aka kama John Michael Obi kan hanyarsa zuwa gida, bayan ya taso daga bakin aiki.

Satar mutane domin neman kudin fansa ba sabon abu bane a Najeriya, amma galibin barayin sun fi auna shugabannin kamfanonin hakar mai ko ma’aikata a yankin Niger Delta mai fama rigingimu.

Idan za a iya tunawa a 2008 ma an kama ‘dan uwan wani dan wasan kwallon kafa Joseph Yobo, a birnin fatakwal. Shi ma Yobo wata kungiyar kwallon kafa ta a Ingila yake yi wa wasa. Babu tabbas ko an biya kudin asa kamin sakin dan’ uwan nasa bayan ‘yan kwanaki da kama shi.

XS
SM
MD
LG