Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Julius Maada Bio A Matsayin Sabon Shugaban Kasar Saliyo


Karshenta dai an rantsar da Julius Maada Bio a matsayin sabon shugaban kasar Sierra Leone bayanda ya lashe wani zabe mai zafi da aka kamalla.

An rantsarda Julius Maada Bio 12 daren jiya Laraba, jim kadan bayan hukumar zaben kasar ta tabbatar da sunnan sa a matsayin wanda ya lashe zaben kasar a zaben da aka gudanar Asabar din da ta gabata.

Bio, wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar a karkashin lemar jam’iyyar SPP kuma tsohon shugaban sojan kasar, ya lashe zaben da kusan kashi 52 na kuri’un da aka kada. Ya samu nasara ne bayanda ya kada tsohon ministan harkokin waje Samura Wilson Kamara na jam’iyar APC, wanda ya samu kashi 48 cikin 100 na kuri’un.

Bio, wanda kamfe din sa ya tsaya kan akidar kawar da cin hanci da rashawa, shine zai gaji shugaba Ernest Bai Koromo na jam’iyar APC wanda yayi wa'adi biyu yana shugabancin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG