Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Gidajen Mai 23, Da Ake Zargi Da Laifuffuka Daban Daban


Akwai hukunci rufe gida mai na wata 2, da cin tara Naira 100.000, ga wadanda sunka sayarda man fiye da farashi Gwamnati

Hukumar kula da hada hadan man fetur ta kasa dake jihar Filato, ta rufe gidajen mai 23, wadanda take zargi da laifuffuka daban daban.

A cewa babban jami’I mai sa ido kan harkar Man a jihar Filato, Mr Douglas,11, daga cikin gidajen man da aka rufe suna da lasisi kuma suna siyarda man ne fiye da farashin da Gwanati ta kayyade.

Ya ce akwai hukunci rufe gida mai har na tsawon watani 2, da cin tara Naira 100.000, ga wadanda sunka sayarda man fiye da farashi Gwamnati.

Sai dai a ‘yan kwanakin nan matsalar karanci mai yayi Kamari a wasu jihohi na arewacin Najeriya.

Shugaban kungiyar direbobi masu dakon man fetur na jihar Filato, Alhaji Danladi Muhammad, yana mai cewa akwai rashin kaya ne a Calabar da Lagos inda ake daukan kayan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

XS
SM
MD
LG