Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rushe Majalisar Dokoki tare Da Dakatar Da Aiki Da Tsarin Mulki A Masar


Firayim minista Ahmed Shafiq yana ganawa da 'yan jarida, lahadi 13 Fabrairu 2011 a birnin al-Qahira.

Sojojin da suka amshi mulki bayan hambarar da Hosni Mubarak sun ce zasu ci gaba da jan ragamar mulki har zuwa zabe a watan Satumba

Rundunar sojojin Masar ta rushe majalisar dokoki, ta kuma dakatar da yin aiki da tsarin mulki, biyu daga cikin muhimman bukatun masu zanga-zangar neman dimokuradiyya a bayan tunzurin kwanaki 18 da ya hambarar da shugaba Hosni Mubarak daga kan mulki.

A yau lahadi, shugabannin sojojin da suka karbi mulki a bayan da Mr. Mubarak yayi murabus ranar Jumma’a suka bayar da sanarwar cewa zasu mulki kasar har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe a watan Satumba.

Sun bayarda wannan sanarwa jim kadan a bayan da firayim minista Ahmed Shafiq na Misra yace babban aikin dake gaban majalisar ministocinsa mai samun goyon bayan sojoji shi ne maido da tsaro da kuma rayuwa irin ta yau da kullum a kasar. Shafiq yana magana ne yau lahadi a taron ‘yan jaridarsa na farko tun saukar da Mr. Mubarak yayi ranar jumma’a.

Mr. Mubarak ya nada Mr. Shafiq a zaman firayim minista a ranar 29 ga watan Janairu, kwanaki 4 a bayan da aka fara gudanar da zanga-zangar.

Mr. Shafiq yace manyan gurorin gwamnati na dogon lokaci sun hada da maido da ci gaba da samun kayayyakin bukatu na yau da kullum da inganta ilmi a kasar.

Su ma sabbin sojoji masu shugabancin Masar sun yi kokarin maido da rayuwa irin ta yau da kullum yau lahadi a al-Qahira, inda suka tura dakaru domin kawar da sansanonin da ‘yan rajin dimokuradiyya suka kafa a dandalin Tahrir domin ababen hawa su samu hanyar shigewa ta wannan dandali da ya zamo tungar masu tunzuri.

Daruruwan dubban Misrawa sun yi bukukuwan murnar hambarar da Mr. Mubarak a wannan dandali na Tahrir a ranakun jumma’a da asabar kafin su koma gidajensu, amma har yanzu akwai daruruwan mutane a dandalin, su na masu lasar takobin ci gaba da zama a can har sai sojoji sun biya bukatunsu na gabatar da sauyin dimokuradiyya. An taba ‘yar kokawa a lokacin da wasu daga cikin wadannan ‘yan raji suka yi kokarin hana sojoji kawar da sansanonin da aka kafa a wurin.

A wasu sassan birnin na al-Qahira kuma, daruruwan ‘yan sanda sun yi zanga-zanga a kofar ma’aikatar harkokin cikin gida, su na bukatar karin albashi tare da ladabtar da jami’an ma’aikatar da suka ce su na bata musu suna. Sojojin dake gadin ma’aikatar sun yi harbin gargadi a sama.

XS
SM
MD
LG