Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan sandan kasar Masar sun yi arangama da masu zanga zanga a kudancin kasar


Ma'aikatan hukumar sufurin jiragen ruwa a Suez da suka fara yajin aikin jiya.

An kashe mutane uku a wata arangama tsakanin jami'an tsaron kasar Masar da masu zanga zanga a kudu maso yammacin kasar.

Arangama tsakanin jami’an tsaron kasar Masar da masu zanga zanga a kudu maso yammacin kasar ya yi sanadin kashe mutane uku wasu da dama kuma suka jikkata, a tashin hankali na baya bayan nan dake da alaka da tarzomar, da Majalisar Dinkin Duniya tace ya yi sanadin mutuwar sama da mutane dari uku tun da aka fara zanga zangar ranar ashirin da biyar ga watan Janairu. Masu zanga zanga da dama a yankin New Valley sun ji raunuka yayin arangamar da aka yi ranar Talata da kuma jiya Laraba. A birnin Suez Canal, daruruwan mutane sun cinnawa gidajen gwamnati wuta domin nuna fushinsu kan batun gidaje. A birnin Alkahira kuma, dubban mutane sun ci gaba da dafifi a dandalin Tahri da zumar ganin shugaba Hosni Mubarak ya sauka daga karagar mulki. Masu zanga zanga sun maida dandalin ya zama wani sansani inda aka tanada wuraren jinya da cajin wayoyin salula da wuraren kade kade har da tashar radio. Sun kuma kebe wani wuri domin karrama wadanda suka kashe a tashin hankalin dake da nasaba da zanga zangar, inda aka lillika hotunan mamatan da kuma wadansu abubuwan tunawa. Jiya Laraba ministan al’adu na kasar Masar Gaber Asfour ya yi murabus kwana tara bayan karbar mukamin a sabuwar gwamnatin Mr. Mubarak. Asfour yace yayi murabus ne bisa dalilan rashin lafiya.

XS
SM
MD
LG