Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Sandan Iran Sun Harba Barkonon Tsohuwa kan Masu Zanga-zanga

Masu zanga zanga a kasar Iran.

Yau Litini jami’an tsaron Iran sun harba barkonon tsohuwa don su fasa taron dubban Iraniyawa masu shirin gangamin nuna goyon baya ga zanga-zangar Tunisia da Misra.

Yau Litini jami’an tsaron Iran sun harba barkonon tsohuwa don su fasa taron dubban Iraniyawa masu shirin gangamin nuna goyon baya ga zanga-zangar Tunisia da Misra.

Shaidun gani da ido sun ce ‘yan sandan kwantar da tarzoma, wadanda da yawansu ke bisa Babura, sun yi ta shawagi a tsakiyar Tehran, a daidai lokacin da kungiyoyin adawa ke shan alwashin kaddamar da gangaminsu duk ko da kin yadda da gwamnati ta yi da takardarsu ta neman izini.

Jami’an tsaro sun bazu bisa titunan Tehran sun kuma tare hanyar zuwa gidan wani shugaban ‘yan adawa.

XS
SM
MD
LG