Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga zanga da yajin aiki sun bazu a kasar Masar


Ma'aikatan hukumar sufurin jiragen ruwa a Suez da suka fara yajin aikin jiya.

Kanfoni da suka hada da na yawon bude ido da masaku da jiragen da kuma ma'aikatun gwamnati sun shiga yajin aikin gama gari.

An shiga yajin aikin gama gari da ya kunshi ma’aikatan ayyukan yawon bude ido, da masaku, da na jiragen kasa da kuma na gwamnati, a duk fadin kasar Masar jiya Laraba, yayinda ‘yan hamayya ke daukar wani sabon salo a kamfen din neman sauke shugaba Hosni Mubarak daga karagar mulki bayan ya shafe shekaru talatin yana shugabanci. Sama da ma’aikata dubu shida suka yi zanga zanga a rana ta biyu jiya Laraba, domin nuna rashin amincewarsu da rashin ingancin albashi a kamfanoni biyar mallakar hukumar sufurin ruwa ta Suez, wadda ta kasance ginshikin tattalin arzikin kasar Masar. Ma’aikatan masaku dubu biyu sun yi zanga zanga a Suez yayinda dubban mutanen da koma bayan harkokin yawon bude ido ya shafa, sun yi zanga zanga a Luxor. Daruruwan wadanda ke zaune a gidaje marasa galihu a mashigin ruwan Suez sun cinnawa shelkwatar gwamna wuta, domin nuna fushinsu a kan rashin matsuguni. An kuma yi zanga zangar kin jinin Mubarak da ya yi sanadin rasa rayuka a hamadar Kharga wadda ke tazarar kilomita dari shida da kudancin Alhakira. Yayinda masu zanga zanga zanga suka koma ofishin ‘yan sanda da kuma wadansu gine ginen gwamnati. Wannan ta faru ne yayinda jarida mafi girma a kasar, al-Ahram ta dawo rakiyar gwamnati. Jiya Laraba shafin farko na jaridar, wanda ya shafe kwanaki baya ba zanga zangar fifiko, ya bayyana hare haren da magoya bayan Mubarak suke kaiwa a dandalin Tahrir a matsayin “yiwa kasa laifi”.

XS
SM
MD
LG