Accessibility links

An Sace Ma'aikatan Jirgin Ruwa A Gabar Najeriya


Mayakan ruwa su na binciken wani jirgin ruwan da ake zaton na 'yan fashi ne a mashigin ruwan Guinea, kusa da gabar Najeriya

A ranar alhamis da ta shige aka kai farmaki a kan wannan jirgin ruwan daukar kwantwena, kilomita 80 daga tashar Brass dake Jihar Bayelsa.

Wata kungiya mai sanya idanu kan fashin jiragen ruwa a cikin teku, ta ce wasu ‘yan fashi dauke da muggan makamai sun sace ma’aikata 5 na wani jirgin ruwa a dab da gabar Najeriya.

Kungiyar mai suna IMB a takaice, ta ce a ranar alhamis da ta shige aka kai farmaki a kan wannan jirgin ruwan daukar kwantwena, kimanin kilomita 80 daga tashar Brass dake Jihar Bayelsa a Najeriya.

Kungiyar ta ce ‘yan fashi su 14 dake tafiya cikin wani kwale-kwale mai sauri tare da wani jirgin ruwansu na jigilar kaya, sun shiga cikin jirgin ruwan na kwantena suka sace biyar daga cikin ma’aikatansa, suka bar sauran ba tare da ko kwarzane ba.

Rahoton yace ‘yan fashin sun kuma sace kudi daga jirgin da ma’aikatansa.

Kungiyar IMB ta ce rashin tabbatar da bin dokokin zirega zirgar jirage ya taimaka wajen karuwar yin fashi cikin teku a gabar Najeriya da kuma yankin mashigin ruwan Guinea a cikin ‘yan shekarun nan.

Kungiyar ta ce yawan fashe-fashen jiragen ruwa ya karu daga sau 10 a shekarar 2011 zuwa 27 shekarar da ta shige.
XS
SM
MD
LG