Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattaunawar Gumi Da 'Yan Ta'adda Ba Alheri Ba Ne - Dattawan Arewa


Sheik Ahmed Gumi Tare Da Fulani Yan Bindiga.
Sheik Ahmed Gumi Tare Da Fulani Yan Bindiga.

Kungiyar Dattawan Arewa ta yi kira ga malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi da ya gaggauta dakatar da ziyarar da yake yi a sansanonin 'yan ta'adda.

Kungiyar ta Dattawan Arewa ta bayyana korafi akan ziyarce-ziyarcen da Sheikh Ahmad Gumi ya ke yi a sansanonin ‘yan ta’adda da sunan shugabantar sulhu tsakanin gwamnati da ‘yan ta da kayar bayan.

A ‘yan makwannin nan ne Sheikh Gumi ya shiga gudanar da taruka da ‘yan bindiga a jihohin Arewa maso yamma bisa kashin kan sa, inda kuma ya yi kira ga gwamnati da ta yi afuwa ga ‘yan bindigar.

Dandalin na dattawan Arewa yana mai da martani ne akan wasu kalamai da aka ce malamin addinin yayi, inda ya ke dora alhakin yawaitar ayukan ta’addanci a Arewacin Najeriya da yadda Kiristocin sojojin kasar suke kakkashe masu ta da kayar baya a yankin.

Haka kuma an zargi Gumi da furka kalaman tunzurawa a lokacin da yake jawabin sasantawa da ‘yan bindiga domin sakin daliban makarantar sakandare ta Kagara a jihar Naija.

A wata sanarwa da kungiyar ta Dandalin Dattawan Arewa ta fitar mai dauke da sa hannun babban jami’inta na kasa Injiniya Zana Goni, ta yi kira ga shehin malamin da ya daina wannan rangadin da ke “kara hura wutar tashin hankali a Arewa”, domin kuwa sun tamke damarar hana duk wani yunkuri na disashe kokarin da dakarun kasar ke yi na yaki da ta’addanci.

Sanarwar ta ce kalaman da malamin ke furtawa tamkar “kara wa ‘yan ta’adda kwarin gwiwa” ne akan abin da suke yi.

Kungiyar ta bayyana mamakin yadda "malam Gumi ya dauki bangare", bayan fitowa da shirin na sa na tattaunawa da ‘yan ta’adda, tana mai cewa abinda ya ke yi tamkar “jefa rayukan sojojin da ba Musulmai ba ne a cikin mummunan hatsari.”

Karin bayani akan: Sheikh Ahmed Gumi, Fulani, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG