Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 6 Tare Da Sace Wasu 15 A Jihar Neja


Makaman da aka kama a Zamfara
Makaman da aka kama a Zamfara

Wasu ‘yan bindiga dauke da manyan bindigogi sun sake kai wani sabon hari da ya hallaka mutum akalla 6 a jihar Neja da ke arewacin Najeriya.

An kai karin ne a yankin Tungan Makeri inda aka ba da labarin kashe mutum 4.

Sai kuma kauyen Yakila dukkanin su a yankin karamar hukumar Rafi, inda shi kuma aka kashe mutum 2 tare da yin awon gaba da wasu Mutane 15.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun yi dirar mikiya ne a wadannan kauyuka guda 2 dauke da manyan bindigogi da sanyin safiyar ranar Asabar.

Wannan hari dai yana zuwa ne a daidai lokacin da aka kubutar da daliban makarantar sakandaren kimiyya ta garin Kagara da ke karamar hukumar Rafi da safiyar ranar Asabar.

A lokacin da wakilin VOA ya tuntunbi kakakin ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun a kan wannan sabon harin ya ce zai yi bincike kafin ya yi bayani a kan lamarin.

Shi ma Sakataren Gwamnatin Jihar Nejan wanda shi ne shugaban Kwamitin Harkokin Tsaron Jihar, Alhaji Ahmad Ibrahim Matane, ya ce ba shi da cikakken bayani a kan sabon harin, amma idan suka kammala binckike za su yi ma manema labarai karin bayani.

Jihar Neja dai tana fama da hare-haren 'yan bindiga da satar mutane, inda ko a ranar 22 ga watan Fabrairu sai da aka sako fasinjojin motar NTSA da aka yi garkuwa da su.

XS
SM
MD
LG