Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Shugaban Majami'ar Methodist Ta Najeriya Da Aka Sace


Shugaban Cocin Methodist a Najeriya, Samuel Kanu Uche
Shugaban Cocin Methodist a Najeriya, Samuel Kanu Uche

Shugaban Cocin Methodist a Najeriya ya samu ‘yancinsa kwana guda bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da shi a kudu maso gabashin kasar, kamar yadda ‘yan sanda suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press da yammacin ranar Litinin.

An yi garkuwa da Samuel Kalu Uche ne a ranar Lahadin tare da wasu manyan malaman coci guda biyu a kan wata babbar hanya a yankin Umunneochi da ke kudu maso gabashin jihar Abia. Kakakin rundunar ‘yan sandan Geoffrey Ogbonna, ya ce an sako limaman biyun, amma bai bayar da cikakken bayanin sakinsu ba.

Duk da cewa sace-sacen ya fi kamari a yankin arewa maso yammacin Najeriya mai fama da rikice-rikice, shi ma yankin kudu maso gabas na fama da munanan hare-hare a 'yan shekarun nan. Hukumomin kasar dai na zargin 'yan kungiyar masu fafutukar neman kafa kasar Biafra da hannu wajen kai hare-hare da dama.

Najeriya ita ce kasa mafi yawan al'umma a Afirka kuma sace-sacen da ake yi don neman kudin fansa ya zama abun takaici.

Kungiyar Kiristocin Najeriya ta yi Allah-wadai da sace sacen tare da yin kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya kawo karshen satar malamai da sauran ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba.

Idan har za a iya yin garkuwa da wani babban limami irinsu Uche kamar wani jariri dan shekara uku a kan babbar hanya ba tare da wata turjiya daga ‘yan sanda ba, to lalle wannan na nuni ga yadda tsarin tsaron mu ya zama.” Inji kungiyar.

~AP

XS
SM
MD
LG