Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Dogayen Layuka A Rumfunan Zaben Amurka


Layin zabe a jihar Virginia
Layin zabe a jihar Virginia

Yau Talata ne Amurkawa ke zuwa rumfunan zabe a fadin kasar don zaben sabon ko sabuwar shugaban kasa.

Biyo bayan yakin neman zabe mai tsawo, mai zafi kuma da 'yan takarar neman shugabancin Amurka sukayi, yar takarar jam’iyyar Democrat Hillary Clinton da Donald trump na jam’iyyar Republican sun yi kira na karshe ga magoya bayansu.

Clinton ta kira wannan zaben a matsayin babban gwaji, yayinda shi kuma Trump ya ayyana ranar a matsayin ta samun ‘yanci. Dukkansu sunyi bayani a safiyar yau Talata, ranar da ta zamo ta karshe wajen yakin neman zaben su, mai cike da abubuwan kuma tun daga daren jiya.


A lokacin da suke gudanar da tarurrukan---Clinton a jihar North Carolina shi kuma Trump a jihar Michigan, aka sami sakamako daga kuri’un farko da aka kada a rumfunan zabe. Clinton ta sami yawancin kuri’un da aka kada a garin Dixville Notch dake jihar New Hampshire, inda ta sami galaba akan trump da kuri’u 4 shi kuma yana da 2.


An ga dogayen layuyyuka a safiyar yau a wurare kamar Virginia da New York a lokacin da aka bude rumfunan zabe.

XS
SM
MD
LG